Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi ‘yan majalisar tarayya takwas da suka sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC a wani taro da aka gudanar a majalisar tarayya da ke Abuja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Dawakin-Tofa, ya fitar a Kano a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa sauya shekar ta biyo bayan rikicin cikin gida da ke addabar NNPP.
‘Yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Tijjani Abdulkadir Jobe, Garba Ibrahim Diso, Hassan Shehu Hussain, Idris Dankawu, Muhammad Chiroma Nalaraba, Rabiu Yusuf, Dr Ghali Mustapha Tijjani da Muhammad Bello Shehu.
A wajen taron, an samu halartar wasu manyan jiga-jigan APC ciki har da tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan sauyi wani bangare ne na tsarin dimokuradiyya, yana mai cewa sauya sheƙa abu ne da ake samu a cikin tsarin siyasa mai inganci.
Ya kuma jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar Kano, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
Haka kuma, ya yi kira ga hadin kai da hadin gwiwa tsakanin zababbun shugabanni domin tabbatar da ci gaban jihar baki daya.













































