Kano: Gwamnati ta dakatar da Sheikh Lawan Triumph daga yin wa’azi har sai an kammala bincike

WhatsApp Image 2025 10 01 at 16.26.49 750x430

Majalisar Shura ta jihar Kano ta dakatar da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Lawan Triumph, daga yin wa’azi da hudubobi a bainar jama’a har sai an kammala bincike kan korafe-korafen da aka gabatar a kansa.

Wannan bayani ya fito daga sakataren majalisar, Malam Shehu Wada Sagagi, a ranar Laraba.

Sagagi ya bayyana cewa majalisar ta karɓi korafe-korafe daban-daban da ake zargin malamin da yin furuci marasa dacewa game da Annabi Muhammad (SAW).

Sai dai ya ce wasu daga cikin koke-koken ba su da wata hujja, don haka aka yi watsi da su.

A cewarsa, korafe-korafen da aka gabatar da hujjoji cikinsu ciki har da bidiyo kuma an bincike su da kyau, sannan kwamitin ya fitar da cikakken rahoto bisa sakamakon da suka samu.

Majalisar ta ce Sheikh Lawan Triumph bai samu gayyata domin kare kansa ba tukuna, amma za a kira shi nan gaba domin ya bayyana matsayinsa.

Labari mai alaƙa: Zargin ɓatanci ga Annabi: Majalisar Shura ta Kano ta gayyaci Sheikh Lawan Triumph da masu ƙorafi

Don cimma hakan, an kafa wani kwamiti na mutum bakwai da zai dauki nauyin gayyatar sa tare da tabbatar da cewa shari’ar ta kasance a fili kuma jama’a sun samu labarinta ta kafafen watsa labarai.

Rahotanni sun nuna cewa cece-kucen ya samo asali ne daga zargin cewa malamin ya yi wasu kalamai kan haihuwar Annabi (SAW), tsaftarsa da kuma iyayensa, wadanda aka ɗauka a matsayin sabawa ka’idojin Musulunci.

Saboda haka gwamnatin jihar ta mika batun ga majalisar Shura wacce ake darajata, domin ta bayar da shawara bisa shari’ar Musulunci.

Sagagi ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa duka bangarorin biyu, malamin da masu kara, za a ba su dama iri ɗaya wajen kare kansu.

Ya kuma tabbatar da cewa haramcin wa’azin na dan lokaci ne, har sai an kammala binciken cikin gaskiya da adalci.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here