Tsoffin shugabannin kasa marigayi Muhammadu Buhari da Umaru Musa Yar’adua sun shiga cikin jerin fitattun mutane da aka wallafa a wani littafi da ke dauke da sunayen manyan ‘yan Najeriya daga jihar Katsina.
Littafin mai taken “100+ Eminent Nigerians from the Katsina State: Profiles in Nation Building and History, Volume One” an kaddamar da shi ne a Katsina ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa, mai taimaka wa shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir-Masari ne ya kaddamar da littafin.
An wallafa shi domin girmama mutanen Katsina da suka bayar da gudunmawa a ci gaban jihar da kasa baki ɗaya.
A jawabinsa, gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce ba wai kawai kaddamar da littafin aka yi ba, illa ma ya kamata matasa su karanta shi domin su koyi darussa daga rayuwar wadanda aka ambata a ciki.
Ya ce littafin ya zama abin daraja da za a rika riƙewa tare da yin koyi da kyawawan dabi’u na fitattun mutanen da ke cikinsa.
Shi ma sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, ya bayyana littafin a matsayin muhimmin takarda mai cike da kwarin gwiwa da nishadantarwa, saboda ya tattaro bayanai kan fiye da mutane 100 daga Katsina da suka taka muhimmiyar rawa a ci gaban kasa da jihar.
A nasa bangaren, mai nazarin littafin, Dr. Aliyu Rabiu-Kurfi, ya bayyana shi a matsayin abin tarihi da za a dinga tunawa da shi.
Ya ce, yayin da jihar Katsina ta cika shekaru 38 da kafuwa, wannan littafi mai shafuka 600 ya kasance abin tunawa da kuma taswira da za ta jagoranci matasa wajen samun kima da muhimmanci a nan gaba.
NAN













































