Tsohon shugaban kungiyar kwadago, Frank Kokori, ya rasu yana da shekaru 80

Mr. Frank Kokori  750x430 (1)
Mr. Frank Kokori 750x430 (1)

Tsohon sakataren kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa NUPENG Frank Kokori ya rasu.

Kokori ya rasu ne yana da shekaru 80 a duniya, bayan shafe wata guda yana kwance a asibitia.

Rahotannin sun bayyana cewa ya rasu ne a asibiti mai zaman kansa da ke Warri da misalin karfe 1:30 na daren Alhamis, 7 ga watan Disambar 2023, wanda ya yi daidai da ranar haihuwarsa.

Mataimaki na musamman ga Kokori, Atawada Oke, shi ne ya bayyana wa manema labarai rasuwar marigayin.

Tuni dai manyan baki da suka hada da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege da jami’an NUPENG sun je ta’aziya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here