A jiya ne sabon ministan tsaron kasar Laberiya ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon zanga-zangar da matan aure da zawarawan sojojin da suka rasu suka yi na nuna adawa da nadin nasa, kamar yadda shafin intanet mai zaman kansa na Daily Observer ya rawaito.
Murabus ɗin Price Charles Johnson ya zo ne kwanaki biyu bayan da matan suka bai wa shugaba Joseph Boakai wa’adin sa’o’i 24 da ya kori ministan sakamakon cin zarafin da ya yi wa sojoji a lokacin da yake shugabantar sojoji tsakanin shekarar 2018 zuwa farkon wannan shekara.
Karanta wannan: “Mun biya albashin ma’aikata na Janairu” – Gwamnatin Tarayya
Matan da zawarawan sun yi nuni da karancin albashi da rashin tsaro da karancin wutar lantarki da kuma almundahana a tsakanin sojoji.
A cikin wasikar murabus din, ministan ya ba da misali da rikicin siyasa da na jama’a da ke faruwa a halin yanzu sakamakon zanga-zangar da matan suka yi.
An nada Johnson a farkon wannan watan ne.