
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta biya dukkan ma’aikata albashinsu na watan Janairu.
Manyan jami’ai a ma’aikatan Gwamnatin Tarayya OHoCSF da zaɓaɓɓun ma’aikatu da hukumomi na gwamnati ne suka shaidawa jaridar Daily Trust hakan, inda suka ce sun yi mu’amala da wasu ma’aikata da abokan aikinsu kuma suka tabbatar musu da cewa sun ga albashinsu.
Ɗaya daga cikinsu ta ce ta karbi albashinta a daren Lahadi, kuma tun da karfe 11:00 na safiyar Litinin, ba ta ji labarin wani wanda bai karɓi albashinsa ba.
Karanta wannan: “Najeriya Talaka Ce” – Martanin fadar Shugaban Kasa ga Sarkin Kano
Daraktan yaɗa labarai da hulda da Jama’a na Hukumar ta OAGF, Bawa Mokwa ya shaida wa jaridar cewa ofishin ya sa ido a kan yadda lamarin ya faru kuma zai iya tabbatar da cewa duk ma’aikatu da hukumomi da ba su ƙarbi albashinsu ba na watan Janairu sun karɓa yanzu.
Mokwa ya bayyana fatansa cewa ba za’a samu irin wannan jinkirin nan gaba ba.
An daura alhakin jinkirin albashin watan Janairu a kan matsalar fasaha na tsarin biyan albashi na bai ɗaya na gwamnati.