Da ɗumi-ɗumi: DSS ta saki Walida

BREAKING 750x430

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, a daren Laraba ya karɓi Walida Abdulhadi Ibrahim, yarinyar da ta ɓace daga jihar kuma ta kasance a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Gwamnan ya ce duk batutuwan da suka shafi zargin sace ta za a miƙa su gaban kotu domin yanke hukunci, yana mai tabbatar da cewa za a yi adalci.

Ya bayyana cewa Walida ‘yar asalin Jigawa ce, kuma gwamnatin jihar za ta tabbatar da tsaronta da kuma murmurewarta daga duk wata damuwa da ta fuskanta.

Rahotanni sun ce gwamnan ya je hedikwatar DSS da ke Abuja tare da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Aliyu; Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a, Barrista Bello Abdulkadir Fanini; Kwamishinan Harkokin Mata, Hajiya Hadiza Abdulwahab; da Kwamishinan Muhalli, Dr Nura Ibrahim Doka, da sauransu.

Daraktan Janar na DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, tare da manyan jami’an hukumar, sun miƙa Walida ga gwamnan.

Wakilai daga Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), da kungiyar FIDA, kungiyoyin farar hula da ‘yan jarida sun halarta.

Sai dai iyayen Walida ba su halarci wurin miƙa ta ba, wanda ya ɗauki lokaci har zuwa misalin ƙarfe 10:40 na dare.

Walida ta ɓace tun 2023 daga Ƙaramar Hukumar Hadejia ta Jihar Jigawa, inda ake zargin tana hannun wani Mariam kafin daga bisani ta gudu.

Daga baya ta bayyana a Abuja inda aka ce tana zauna tare da wani jami’in DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi, har ma ta haifi jaririya a watan Nuwamba 2025.

Bayan kokarin iyalanta na karɓo ta ya ci tura, an shigar da ƙorafi a hedikwatar DSS sannan aka garzaya kotu a Jigawa.

Kotun ta umarci a miƙa ta ga iyayenta, amma DSS ta shigar da ƙorafin ƙalubale tana mai cewa tana gudanar da bincike.

Bayan wallafar wani rahoto kan lamarin, kungiyoyi daban-daban sun nuna damuwa kan ci gaba da riƙe ta a hannun DSS.

Da yake jawabi, Gwamna Namadi ya ce Walida za ta kasance karkashin kulawar gwamnatin jihar har sai an warware duk takaddamar da ke tattare da lamarin.

Ya ƙara da cewa jaririyar da ta haifa ma za ta kasance karkashin kulawar gwamnatin jihar.

Da yake jawabi daraktan janar na DSS Adeola Oluwatosin Ajayi, ya mika Walida ga gwamnatin.

A ranar Litinin, wata haɗakar ƙungiyoyi da ta ƙunshi reshen Abuja na (MURIC), da (FOMWAN), da (MSO), da kuma Women in Da’awa, sun gudanar da taron manema labarai na duniya a Abuja inda suka buƙaci a mayar da Walida zuwa wani wuri mai zaman kansa (neutral ground).

Da yake magana a madadin haɗakar ƙungiyoyin Walida Abdulhadi, Ustaz Yunus Salahudeen ya ce batun ya wuce maganar addini kawai, yana shafar manyan batutuwa na adalci, tsarin mulki da kuma haƙƙin ɗan Adam.

Ya tuna cewa shi ne Daraktan DSS na Jihar Bayelsa a lokacin da aka yi zargin sace Ese Oruru.

Ya yi korafin cewa wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa sun yi amfani da lamarin wajen rura wutar rikici da tayar da kura, inda ya ce Ifeanyi na tsare.

Daraktan Janar na DSS ya kuma ce har yanzu Ifeanyi yana tsare a hannun hukumar, kuma ba za a kyale shi ba idan aka same shi da laifi.

Ya ce zai fuskanci hukunci idan bincike ya tabbatar da laifinsa, yana mai cewa suna da dokoki da ke jagorantar ayyukansu.

Barrista Haroun Muhammad ya ce Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya ta shiga lamarin Walida ne domin rage tashin hankali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here