HOTUNA: Al’ummar Jigawa na neman agajin gaggawa kan tabarbarewar Cibiyar Kulada lafiya

IMG 20230709 WA0058 768x576
IMG 20230709 WA0058 768x576

Cibiyar kula da lafiya dake unguwar Bardo, karamar hukumar Taura, jihar Jigawa

Cibiyar kulada kiwon lafiyar a matakin farko (PHC) da ma’aikata masu kula da duk wani bukatun kiwon lafiya na jama’a sun shiga mawuyacin hali sakamakon rugujewar cibiyar, Mazauna yankin Bardo sama da dubu 40 a karamar hukumar Taura a jihar Jigawa,

IMG 20230709 WA0100 768x576

Wani mazaunin unguwar mai suna Bashir Umar, ya shaida wa SOLACEBASE cewa tabarbarewar fannin kiwon lafiya a matakin farko da ma’aikata guda daya kacal da ke aiki a matsayin ma’aikacin jinya, kuma mai kulawa da duk wasu ayyukan tallafi sun kasance kamar shekaru kusan shida batareda kawo musu dauki ba.

IMG 20230709 WA0097 768x576

“Duk kokarin da muka yi na hukumomi su gyara cibiyar kulada lafiyar dakuma samar mana da ma’aikatan da za su ba mu kulawa ga marasa lafiya sun ki yin wani abu a kan hakan, Umar ya koka.

IMG 20230709 WA0059 768x576 IMG 20230709 WA0059 750x430

Umar wanda ya yi magana da SOLACEBASE a ziyarar da jaridar ta kai wa al’umma kan harkokin kiwon lafiya kwanan nan ya yi amfani da wannan damar wajen rokon hukumomin gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa wa al’umma don inganta harkar kiwon lafiya.

Haka kuma, wata uwa mai yara hudu, Amina Ibrahim ta ce halin da asibitin ke ciki ya taimaka wajen rasuwar kawarta, Hauwa, da ta yi nakuda da daddare kuma ta kasa samun kulawa.

“Muna buƙatar asibiti mai aiki ba dare ba rana, saboda wanda muke da shi yana da ma’aikaci ne guda ɗaya wanda ke kula da duk bukatunmu ba tare da wani kayan amfanin lafiya ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here