Gamayyar wasu ƙungiyoyi a ƙarƙashin Movement Against Corruption in Nigeria (MACIN), ta yi kira ga hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) da Interpol su sanya ido kan tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, domin kada ya gudu ya bar ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar Kabiru Saidu Dakata ya buƙaci NIS da Interpol su sanya ido kan Ganduje saboda yana ɓoyewa a bayan Shugaba Tinubu domin kada a cafke shi inda daga bisani zai yi ƙoƙarin sulalewa daga ƙasar nan.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Ganduje da mutunta doka ya kai kansa wajen hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar domin a bincike shi.
Da yake martani kan kiran da ƙungiyar ta yi, tsohon kwamishinan watsa labarai a gwamnatin Ganduje, Malam Muhammad Garba, ya yi fatali da kiran da ƙungiyar ta yi na Shugaba Tinubu ya nesanta kansa da tsohon gwamnan.
Garba ya bayyana cewa shugaban ƙungiyar, Kabiru Saidu Dakata, wanda ɗan jam’iyyar PDP ne ya koma NNPP a yanzu yana fakewa ne da ƙungiyar kawai domin caccakar gwamnatin Ganduje da ta gabata.
Ya ƙara da cewa ba a daɗe ba da jin Dakata a kafafen watsa labarai yana neman samun muƙami a gwamnatin NNPP ta jihar Kano, inda aka ɗauki nauyinsa ya bayyana a gidan talbijin na Arise TV domin goyon bayan rusau ɗin da gwamnatin NNPP ta ke yi a Kano.