Binani ta shigar da sabuwar ƙara a kan INEC bisa soke sanar da ita a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamnar Adamawa

Sen. Aishatu Binani 679x430 1
Sen. Aishatu Binani 679x430 1

Ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa, Aisha Dahiru Binani, ta shigar da kara a kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan soke bayyana sunanta da ta yi a matsayin wacce ta lashe gwamnar jihar Adamawa

Binani, ta bakin lauyanta, Michael Aondoaka, SAN, ta shigar da sabon karar a gaban mai shari’a Donatus Okorowo na wata babbar kotun tarayya dake Abuja.

Binani, a cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/935/2023, ta kai karar INEC, jam’iyyar PDP da dan takararta, Gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin waɗanda ake kara na 1, 2 da na 3.

Binani na neman a canja hukuncin da INEC ta yanke na yin mi’ara-koma-baya, bayan tun da fari ta sanar da ita a matsayin wacce ta lashe zaben da dakataccen kwamishinan zabe na jihar Adamawa (REC), Hudu Yunusa-Ari.

Aondoaka, yayin da yake gabatar da ƙorafin a yau Litinin, ya bayar da hujjar cewa kotun sauraron kararrakin zabe ce ke da hurumin yanke hukunci kan makomar wanda yake karewa kamar yadda sashe na 149 na dokar zabe, 2022 ya tanada.

A cewarsa, hukuncin da INEC ta yanke zai hana Binani yancin ta na sashi na 285(6), wanda ya bada damar kwanaki 18 kafin wa’adin ƙorafin da a ka shigar ya kare a ranar 6 ga watan Mayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here