Hukumar kula da famshon ƴan sanda ta kasa ta shirya wani taron horaswa na kafin ritaya ga jami’an ’yan sanda da ake sa ran za su yi ritaya a shekarar 2026 a yankin Arewa maso yamma.
An gudanar da taron a Kano domin wayar da kan jami’an kan cike takardu da bin hanyoyin da suka dace don tabbatar da sauƙin aiwatar da biyan fansho.
Kwamishinan ’yan sanda mai kula da fansho, Sani Doki-Yusuf, ya bayyana cewa an tsara taron ne domin tunatar da jami’an da ke gab da ritaya muhimmancin kammalawa da sabunta dukkan bayanan fanshonsu, domin kauce wa jinkiri ko matsaloli wajen biyan hakkokinsu bayan barin aiki.
Ya bayyana cewa yawancin tsofaffin jami’an suna fuskantar ƙalubale ne sakamakon rashin cikawa ko sabunta bayanan su, lamarin da ke haddasa jinkirin biyan fansho.
Ya ƙara da cewa ana sa ran fiye da jami’an ’yan sanda 5,000 za su yi ritaya a shekarar 2026.
Daraktar hukumar fansho ta rundunar ’yan sandan Najeriya kuma jami’ar inshorar rundunar, ACP Lydia Ameh, ta jaddada muhimmancin shirin wayar da kan jami’an.
Ta ce shirin na kawo bayanan fansho kai tsaye ga masu ritaya, tare da tabbatar da sun fahimci yadda za su sabunta bayanai da karɓar hakkokinsu ba tare da wahala ba.
Ta bayyana cewa sakamakon jajircewar babban sufeton ’yan sanda, jami’an da suka kammala cika takardunsu yadda ya dace na iya karɓar fanshonsu cikin kwanaki uku zuwa biyar na aiki.
Ta yaba da yadda aka bai wa jin daɗin jami’an da ke aiki da waɗanda suka yi ritaya muhimmanci, tare da tallafa wa iyalan jami’an da suka rasu.
Babban daraktan kamfanin fansho na rundunar ’yan sandan Najeriya, Abdulkarim Shehu-Gezawa, ya bayyana cewa tun kafa kamfanin an biya tsofaffin jami’an 30,370 kuɗaɗen fansho da suka kai Naira Biliyan 97.5, yayin da aka biya Naira Biliyan 39.5 a matsayin diyya ga ’yan uwa 8,847 na jami’an da suka rasu.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu tsofaffin jami’an 25,572 na karɓar kusan Naira Biliyan 1.5 a kowane wata a matsayin fansho.
Ya kuma bayyana cewa tsarin fansho na gudummawa da ake amfani da shi a Najeriya yana bin dokar gyaran fansho ta 2004 da aka yi wa kwaskwarima a 2014, tare da ƙa’idojin hukumar kula da fansho ta ƙasa.
Taron ya haɗa da jawabai kan lafiyar masu ritaya da kuma darussa kan ilimin tunanin ritaya, domin shirya jami’an don rayuwa bayan barin aiki.












































