Yayin da ‘yan Najeriya ke cigaba da kokawa kan matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta, mai bawa shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga, ya ce Najeriya kasa ce matalauciya.
Onanuga ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.
“Najeriya kasa ce mai matukar talauci” Inji shi.
Ya kara da cewa, “Ana ganin kamar muna da daraja mai kyau na arzikin kasa, amma kuma kasa ce mai matukar rashin wadatar arziki.”
Karanta wannan: Harin Isra’ila ya lalata masallacin Rafah
Ikirarin Onanuga na zuwa ne sa’o’i bayan Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shaida wa uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu cewa ta sanar da mai gidanta halin da kasar ke ciki wanda ba’a taba ganin irin shi ba.
Har ila yau shugaban kungiyar NLC Joe Ajaero, a ranar Lahadi ya ce NLC na iya neman Naira miliyan 1 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati.
Da yake magana game da manufofin tattalin arziki, Onanuga ya tabbatar da cewa tare da cire tallafin man fetur da kuma hadewar farashin canji, gwamnati na fatan cewa matsin lambar da ake yi wa kudaden kasar zai ragu.