Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Hukumar inshorar ajiya ta Najeriya (NDIC), ta ce za ta fara biyan kudaden inshora ga masu ajiya miliyan 2.3 na bankin Heritage a cikin ruwa a cikin makon nan.
Manajan Daraktan Hukumar NDIC, Mista Bello Hassan ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Karin labari: Majalisar dokoki a Kaduna ta ba da shawarar gurfanar da El-Rufai a gaban kotu
Hassan ya ce bankin na da asusun farko na Naira biliyan 650 da kuma lamuni na Naira biliyan 700.
A cewarsa, kashi 99.9 cikin 100 na masu ajiya na rusassun bankin suna da ma’aunin ajiya na kasa da naira miliyan biyar, yayin da 4,000 kawai daga cikin masu ajiya ke da sama da naira miliyan biyar kamar yadda NAN ta tabbatar.