Majalisar dokoki a Kaduna ta ba da shawarar gurfanar da El-Rufai a gaban kotu

El Rufai, Kaduna, Majalisar, dokoki, shawarar, gurfanar, tsohon, gwamnan, jihar, kotu
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ba da shawarar a gurfanar da tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai a gaban kuliya bisa zarginsa da cin hanci da rashawa a...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ba da shawarar a gurfanar da tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai a gaban kuliya bisa zarginsa da cin hanci da rashawa a gwamnatinsa.

Hakan ya biyo bayan binciken kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa, karkashin jagorancin Henry Zacharia.

A cewar rahoton da Zacharia ya gabatar a ranar Laraba, yawancin rancen da aka samu a karkashin gwamnatin El-Rufai, ba a yi amfani da su wajen manufarsu ba, kuma a wasu lokuta, ba a bi ka’idojin da suka dace wajen samun rancen ba.

Karin labari: Babbar Kotu a Kano ta magantu kan shari’ar Ganduje da matarsa da wasu mutum 6

Don haka kwamitin ya bayar da shawarar gudanar da bincike da gurfanar da tsohon gwamnan da wasu jami’an tsaro da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da ake tuhumarsa da laifin yin amfani da mukami ta hanyar bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba, da karkatar da kudaden jama’a, da kuma kudade.

Cigaba na tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here