Ƴancin kan Najeriya: Tinubu zai yi jawabi ga ƴan ƙasa

Tinubu 2 679x430

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yiwa al’ummar Najeriya jawabi a ranar Laraba da misalin ƙarfe 7 na safe, domin bikin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Ya ce dukkan tashoshin talabijin da rediyo, tare da sauran kafafen yada shirye-shiryen za su haɗa kai da gidan talabijin na ƙasa (NTA) da gidan rediyon tarayya (FRCN) domin watsa jawabin shugaban ƙasa.

Wannan shi ne karo na uku da Tinubu zai yiwa ƙasa jawabi a ranar samun ‘yancin kai tun bayan hawansa kan mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Jawabin shugaban ƙasa a ranar 1 ga Oktoba ya kasance al’ada tun bayan samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekarar 1960.

Ana sa ran shugaban zai tabo halin da ƙasar ke ciki tare da haskaka manufofin gwamnatinsa yayin wannan jawabai na musamman ga al’umma.

A ranar Litinin, gwamnatin tarayya ta sanar da soke baje kolin da aka shirya yi domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Sai dai ta bayyana ranar Laraba a matsayin hutu na musamman domin murnar zagayowar ranar.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da bukukuwa da shirye-shirye na musamman domin tunawa da ranar da Najeriya ta samu cikakken ‘yanci daga mulkin mallaka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here