Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Malam Mele Kyara ya alakanta tsadar gas din girki da ake fama dashi da matsalar karancin man fetur da ake fama dashi a kasuwar duniya.
Kyari ya bayyana hakan a Abuja lokacin bikin bude wani kamfanin gas mai suna Emadeb Energy Services Limited.
Ya ce yanzu haka kamfanin NNPC yana aiki ba dare ba rana wajen ganin an samar da tsare-tsaren da zasu karya farashin gas din girki.
Malam Mele Kyari ya kara da cewa zasu kara adadin gas din da ake samarwa, wanda hakan zai taimawa wajen saukar fashin, yana mai bayyana cewa da zarar tsare-tsaren sun fara aiki al’umma zasu samu sauki wajen siyan gas din.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa yanzu haka a Abuja ana siyar gas 12kg akan naira 8,500 zuwa 9,500, sabanin ‘yan kwanakin baya da ake siya akan naira 4,000 zuwa 6,000.