Tsohon shugaban Hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC ya bayyana cewa jami’ar Ibadan ta cancanci lashe kyautar jami’a ta farko a shekarar 2021 duba da irin ayyukan ci gaban ilimi da jami’ar ta gudanar
Farfesa Peter Okebukola wanda shine ya jagoranci kwamitin tantance jami’o’i da suka fi hazaka ya bayyana hakan ne a wajen taron karawa juna sani da asusun tallafawa makarantun gaba da sakandare TETFund suka shirya a Abuja.
Yace jami’ar ta Ibadan ta duk wasu sharuda da aka shimfida na tabbatar da ingancin karatu da hazakar dalibai, inda tayi zarra cikin jami’o’i 113 da aka tantance.
Ya bayyana asu daga cikin sharudan da aka yi amfani dasu wanda suka hada da yawan daliban jami’a gaba daya da adadin daliban da suka zo daga kasashen ketare da irin gudunmawar da malamai da dalibai suke bayar a shafukan ilimi dake Intanet, har ma da irin yadda jami’o’i ke tallafawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.
Anasa jawabin shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC Farfesa Abubakar Rasheed ya bayyana cewa hukumar zata bunkasa yadda take fitar da jadawalin domin karawa jami’o’i karsashi na gudanar da aiki tukuru domin ganin sun lashe kyautar hukumar.