Gwamnatin tarayya ta saki naira biliyan 50 domin biyan alawus-alawus ga kungiyoyin malamai da na jami’o’in tarayya, inda ta cika wani muhimmin alkawari da shugaba Bola Tinubu ya yi.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Boriowo Folasade ya fitar ranar Laraba.
A cewar sanarwar, sakin kudin ya nuna wani gagarumin mataki na kudurin gwamnatin na sake fasalin fannin ilimi da inganta jin dadin ma’aikatan jami’o’in.
Ya kara da cewa ba da fifikon jin dadin ma’aikatan jami’o’i yana da matukar muhimmanci wajen gina makoma ga daliban Najeriya don su samu ilimi mai inganci.
Karin karatu: Jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 15 a fannin samar da ilimi a matakin farko
Ministan ya kuma yaba da hadin kan kungiyoyin ilimi, inda ya bayyana cewa a halin yanzu kasar na fuskantar daya daga cikin mafi dadewa na zamanin karatu mai tsayi ba tare da katsewa ba a tarihi.
Ya jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da hada kai da duk masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga kowane yaro dan Najeriya.













































