Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya sanar da dakatar da dukkan ayyukansa na zirga-zirga a fadin kasar nan, nan take sakamakon yajin aikin da hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ke ci gaba da yi.
A cikin wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar, ya ce matakin ya zama dole domin NiMet ita ce hukumar da ke da alhakin bayar da rahotannin halin da yanayi ke ciki wadanda ke da matukar muhimmanci ga saukar jirgi lafiya, musamman a wannan lokacin da ake fama da ruwan sama da kuma tsawa.
“A matsayin kamfanin jirgin sama na farko, mun zaɓi yin aiki da gaskiya ta hanyar dakatar da ayyuka har sai NiMet ya dawo da cikakken ayyukan ta.
“Mun fahimci hakan na iya haifar da damuwa, kuma muna ba da hakuri da gaske. Za a tuntubi fasinjoji tare da sabunta musu tikiti,” in ji kamfanin.
Kungiyoyin masana’antu guda uku ne ke goyon bayan yajin aikin, da suka haɗar da kungiyar ma’aikatan kula da zirga zirgar jiragen sama (NUATE), da gamayyar kungiyoyin kula da ayyukan fasaha da walwalar ma’aikata (AUPCTRE) da kuma kungiyar kwararrun matuka jirgin sama (ANAP).
Kungiyoyin a wata takardar da suka aike wa mambobinsu a hukumar sun bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, sun yi namijin kokari wajen ganin an shawo kan matsalar rashin adalci da ake fama da ita, wadda ta kai ga haifar da matsanancin talauci da kuma wahalhalun da ma’aikatan Nimet ke fuskanta, amma sun yi biris da shi.
Kungiyoyin sun kuma koka da cewa an karya yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin mahukuntan Nimet da su tun ranar 29 ga watan Janairun 2025, kan batun gyara wasu sharudda.
Sanarwar ta kara da cewa: “Bisa la’akari da gazawar mahukunta wajen magance matsalolin da muke da su da kuma kasancewar ba za mu iya ci gaba da jurewa wahalhalun da muke ciki ba musamman ganin wa’adin da aka ba hukumar ya kare, ba mu da wani zabi illa mu koma yajin aikin da aka dakatar.
“Saboda haka, an umurci dukkan ma’aikatan Nimet na kasar nan da su janye duk wani aiki daga hukumar tun dags tsakar daren Talata, 22 ga Afrilu, 2025, har sai an samu sanarwa ta gaba.