Kungiyar Gwamnoni ta gana da babban Hafsan soji kan matsalolin tsaro

NGF 2 600x430

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) sun yi wata ganawa da babban hafsan sojin kasa (CDS), Janar Christopher Musa.

Taron na zuwa ne biyo bayan karuwar rashin tsaro da tashe-tashen hankula a sassa da dama na kasar nan.

Taron ya gudana ne domin tattaunawa kan tabarbarewar tsaro a wasu jihohin da kuma shimfida hanyar dakile su.

Taron wanda aka fara shi bayan karfe 9 na dare a Abuja, kuma ya zo ne gabanin taron majalisar tattalin Arzikin ƙasa (NEC) da aka shirya yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasa.

Daga cikin ajandar akwai bukatar a gaggauta magance yawaitar kashe-kashe da barnata dukiyoyi da suka addabi al’umomi a jihohi irin su Filato, Benuwai, Neja, da sauransu, a ‘yan makonnin nan.

Zaman da NGF ta yi da Janar Musa ya nuna yadda ake ƙara nuna damuwa m game da yawaitar hare-hare ta yadda dubban ‘yan Najeriya suka rasa matsugunansu.

Rahotanni sun ce, gwamnonin sun nemi bayanai daga hannun CDS kan ayyukan da sojojin ke yi a halin yanzu, da kuma rawar da gwamnatocin jihohi za su iya takawa wajen tallafawa kokarin sojojin na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Gwamnonin da suka hallarci taron har zuwa lokacin hada wannan rahoto sun hada da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Godwin Obaseki na Edo, Hope Uzodinma na Imo, Dauda Lawal na Zamfara, Seyi Makinde na Oyo, Dapo Abiodun na Ogun, Abdullahi Sule na Nasarawa, da Douye Diri na Bayelsa, da dai sauransu.

Ko da yake ana ci gaba da jiran cikakken bayanin sakamakon taron a hukumance, sai dai masu lura da al’amuran NGF sun bayyana zaman a matsayin “dabara kuma wajibi ne,” musamman idan aka yi la’akari da taron na NEC mai zuwa inda ake sa ran za a gudanar da manyan batutuwan tsaro da shugabanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here