‘Yan bindiga sun hallaka mutane tare da yin garkuwa da wasu a hanyar Kaduna zuwa Zaria

BD6C6E4C D918 4E34 822C 62E379620514
BD6C6E4C D918 4E34 822C 62E379620514

A yammacin jiya litinin ‘Yan bindiga sun yi sun hallaka matafiya da dama tare da yin garkuwa da wasu a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Kofar Gayan dake wajen Zaria.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun rufe hanyar ne da misalin karfe 8 na dare, inda suka fara harbin motoci da mutane, wanda ta haka ne suka samu damar yin garkuwa da mutane.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kwashe mutane da yawa inda suka shiga dasu cikin daji, kafin jami’an tsaro su zo wajen da lamarin ya faru.

Wani da lamarin ya faru a kan idon sa ya ce abu ne mai wuya a iya sanin adadin mutanen da aka yi garkuwa dasu saboda yawan mutanen da abun ya rutsa dasu.

Daya daga cikin wanda ya shaida faruwar lamarin ya ce an kashe wani mutum mai suna Sani Dogara.

Zuwa yanzu rundunar ‘yan sanda bata ce komai kan lamarin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here