Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar aikin babbar hanyar Zaria zuwa Kano da na Dorayi zuwa shatale talen Western Bypass zai kammala a cikin watan Maris din shekara mai zuwa ta 2023.
Babban Daraktan ginawa da gyarawa da kuma lura da aikin manyan hanyoyin kasar nan , na ma’aikatar aiyyuka da Gidaje ta kasa Injiniya Folorunso Benjamin Esan, ne ya bayyana haka a lokacin da yake ziyarar duba yadda aikin yake gudana daga Zaria zuwa Kano, a ranar Juma’a 01 ga watan Yulin 2022.
Folorunso, yace gwamnatin tarayya ta yaba da yadda aikin yake gudana duk da kalubale da ake samu na ababen hawa da ke zirga zirga a hanyar musamman ma a wannan lokaci na Damuna.
Da yake nasa jawabin babban jami’in dake lura da aikin manyan hanyoyin jihohin shiyyar Arewa maso Yamma, Injiniya Adetayo Taiwo, ya ce aikin zai saukaka harkokin sufuri tare da rage yawan hadari, a bangare daya gwamnati zata dauki tsauraran matakan hukunci ga masu lalatawa ko kawo tsaiko a aikin.
Zagayen aikin na tsawon Kilomita 137 daga Zaria zuwa Kano ya duba yadda aikin Titin ke gudana har zuwa shatale talen hanyar Zaria zuwa Dawanau ta Western Byepass mai tsawon Kilomita 26, dake cikin birnin Kano.













































