Kotun kolin Saudiyya ta sanar da cewa za a gudanar da tsayuwar Arafat, a ranar Juma’a 8 ga watan Yuli wanda ke nuna karshen aikin hajjin bana.
Kamfanin dillancin labaran iqna yace, ya nakalto daga shafin kotun kolin kasar Saudiyya na Internet cewa, ranar farko ta sallar Idi za ta kasance Asabar 9 ga watan Yuli.
A cewar sanarwar, an tabbatar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a cibiyar duban wata ta Tamir da ke kusa da birnin Riyadh a yammacin Larabar nan.
Don haka ranar Alhamis 30 ga watan Yuni ita ce ranar farko ga watan Dhul Hijjah.
A baya dai kotun kolin kasar ta yi kira ga daukacin al’ummar musulmin kasar Saudiyya da su duba jinjirin watan Dhu Al-Hijja da yammacin yau Laraba 30 ga watan Zu-Al-Qadah shekara ta 1443 bayan hijira, daidai da 29 ga watan Yunin shekarar 2022.
A wata sanarwa da kotun kolin ta fitar a ranar Litinin din nan ta yi kira ga duk wanda ya ga jinjirin watan da ido ko kuma ta hanyar amfani da na’urar hangen nesa da ya kai rahoto ga kotu mafi kusa da kuma yin rajistar shaida, ko kuma ya kai rahoto ga cibiya mafi kusa don taimakawa wajen isa kotu mafi kusa.
A halin da ake ciki dai kasashen musulmi da dama sun sanar da fara gudanar da bukukuwan Sallah a ranar 9 ga watan Yuli ko kuma 10 ga watan Yuli, dangane da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah da yammacin Laraba.
A ranar 9 ga watan Yuli ne za a yi bikin farko na Idin Al-Adha a mafi yawan kasashen Larabawa da na Musulmi yayin da yawancin kasashen Kudu maso Gabashin Asiya za su fara bukukuwan a ranar Lahadi 10 ga watan Yuli.
Indonesiya, kasa mafi yawan al’ummar musulmi da Malaysia, da Brunei sun sanar da cewa za a fara bukukuwan Sallar Idi a ranar Lahadi, saboda rashin ganin jinjirin watan Dhul Hijjah da yammacin Laraba.
(Saudi Gazette)













































