Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sauya shugaban kungiyar kallon kafa ta Kano Pillars (Sai masu gida) inda ya nada shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima, a matsayin shugaban riko na kungiyar ta Pillars.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Asabar ne kamfanin shirya gasar Firimiyar Najeriya LMC, ya dakatar da tsohon shugaban tawagar ta Pillars sakamakon Marin mataimakin Alkalin wasa da ya yi a wasan mako na 31, tsakanin kungiyar da Dakkada FC.
A sanarwar da sakataren yada labaran gwamna Abba Anwar, ya fitar gwamna Ganduje yace “Lokacin da Kano Pillars ke fuskantar kalubale a gasar Firimiya, ana bukatar jagorancin da zai tafiyar da kungiyar”.
“Don haka Ibrahim Galadima, zai jagoranci tawagar a matsayin riko kafin samar wa da kungiyar sabon shugaba” inji Gwamna Ganduje.
Nadin na Ibrahim Galadima, ya fara aiki ne nan take kamar yadda sanarwar ta tabbatar.













































