Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar “Zuba Jari a Fannin Wutar Lantarki ta Jihohi Uku” da darajar ta ta kai Naira biliyan 50 tare da gwamnatocin jihohin Katsina da Jigawa.
Wannan na cikin sanarwar da kakakin gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, wadda ta bayyana cewa wannan yarjejeniya babbar dama ce wajen tabbatar da tsaron wutar lantarki da bunkasa tattalin arziki a Arewacin Najeriya.
Yarjejeniyar, wadda aka kammala yayin babban taro kan al’amuran wutar lantarki da aka gudanar a Marrakech, Morocco daga 16 zuwa 19 ga watan Oktoba, 2025, za ta baiwa jihohin uku damar kafa kasuwar wutar lantarki ta yankin da samun hannun jari a yunkurin inganta samar da wutar lantarki a Afrika nan gaba (FEA), kuma babban mai zuba jari a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO).
Gwamna Yusuf ya ce wannan hadin gwiwa na da nufin cimma wadataccen wutar lantarki, bunkasa hada-hadar tattalin arziki, da kuma samar da yanayi mai kyau ga masana’antu a Kano da yankin baki daya.
Dr. Gaddafi Sani Shehu, kwamishinan wutar lantarki da makamashi na jihar Kano, ya bayyana cewa wannan shiri zai inganta aikin KEDCO kuma ya bude damar ci gaban tattalin arzikin yankin ta hanyar samar da ingantacciyar wuta da kyakkyawan tsarin gudanarwa.













































