Zaɓen ƙananan hukumomi na FCT: EFCC ta kama mutum 20 kan zargin maguɗin zaɓe, ta ƙwato sama da Naira Miliyan 17

EFCC naira 750x430

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa EFCC sun kama mutane 20 bisa zargin aikata laifukan zaɓe a zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya da aka kammala.

Hukumar ta ce ta kuma ƙwato kuɗi sama da Naira Miliyan 17 da ake zargin an tanade su domin sayen ƙuri’u.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa, ta bayyana cewa an kama mutanen ne ranar Asabar 21 ga Fabrairu, 2026 a sassa daban-daban na birnin.

A cewar ta, an kama mutum biyu a Abaji, tara a Gwagwalada, huɗu a Kuje da kuma huɗu a Kwali.

Hukumar ta ce an kama su ne bisa laifuka daban-daban da suka haɗa da sayen ƙuri’a, sayar da ƙuri’a da kuma hana jami’an zaɓe gudanar da aikinsu, inda jimillar kuɗin da ake zargi ya kai Naira 17,218,700.

An kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da Naira 13,500,000 a cikin mota da aka ajiye kusa da rumfar zaɓe a ƙaramar hukumar Kwali.

Hukumar ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Zaɓen da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu ya gudana a dukkanin ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, wato Abaji, Bwari, Gwagwalada, Kuje, Kwali da Abuja Municipal.

Masu sa ido kan zaɓe sun ruwaito cewa an ga lokutan da ake ba masu zaɓe kuɗi daga Naira 1,000 zuwa Naira 5,000 a wasu rumfunan zaɓe, musamman a Gwagwalada da Kuje.

Sakamakon zaɓen da aka bayyana ya nuna cewa jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi biyar daga cikin shida, yayin da jam’iyyar PDP ta samu kujera ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here