NiMet ta yi hasashen samun yanayin Hazo da gajemare na tsawon kwanaki 3 a faɗin Najeriya

hazy weather 750x430

Hukumar kula da Yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu Hazo a sararin samaniya da gajimare daga ranar Litinin zuwa Laraba a faɗin ƙasar nan.

A rahoton yanayi da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, NiMet ta ce za a samu ɗan ƙura kaɗan a yankin Arewa a ranar Litinin a duk tsawon lokacin hasashen.

Hukumar ta ce wasu jihohi kamar Borno da Yobe za su fuskanci ƙura mai matsakaici, inda hangen nesa zai kasance tsakanin kilomita 2 zuwa 5.

Ta ce a yankin Arewa ta Tsakiya ma za a samu ɗan ƙura kaɗan a duk lokacin hasashen.

A yankin Kudu kuwa, ana sa ran yanayi mai gajimare tare da ɗan hasken rana lokaci-lokaci, tare da ƙaramin yiwuwar tsawa da safe a wasu sassan Cross River da Akwa Ibom.

Ta ƙara da cewa daga baya a rana za a samu tsawa mai ɗauke da ruwan sama kaɗan a sassan Ondo, Ogun, Lagos, Edo, Bayelsa, Cross River, Rivers, Delta da Akwa Ibom.

A ranar Talata NiMet ta yi hasashen ƙura mai matsakaici a yankin Arewa, inda hangen nesa zai kasance tsakanin kilomita 2 zuwa 5.

A Arewa ta Tsakiya kuwa za a samu ɗan ƙura kaɗan.

A Kudu kuma za a samu gajimare tare da hasken rana lokaci-lokaci, tare da yiwuwar tsawa da safe a Akwa Ibom da Cross River.

Daga baya za a samu tsawa mai ruwan sama kaɗan a sassan Lagos, Oyo, Ondo, Ogun, Edo, Bayelsa, Cross River, Rivers, Delta da Akwa Ibom.

Ranar Laraba, hukumar ta ce za a samu ƙura mai yawa a yankunan Arewa da Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.

A Kudu kuma za a samu gajimare tare da hasken rana lokaci-lokaci, da yiwuwar tsawa da safe a Cross River da Akwa Ibom.

Daga baya za a samu tsawa mai tafe da ruwan sama kaɗan a sassan Bayelsa, Lagos, Ondo, Ogun, Edo, Cross River, Rivers, Delta da Akwa Ibom.

NiMet ta shawarci jama’a da su ɗauki matakan kariya saboda ƙurar da ke yawo a sararin samaniya a yankunan Arewa, Arewa ta Tsakiya da kuma jihohin cikin ƙasar a Kudu.

Ta kuma gargadi masu fama da cutar asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka-tsantsan.

Hukumar ta ce direbobi su yi tuƙi a hankali yayin ruwan sama, sannan ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su riƙa samun rahoton yanayi na filayen jiragen sama daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here