Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin gina ƙofofin karɓar kuɗin hanya a manyan hanyoyi guda bakwai da ke shiga cikin birnin Kano, matakin da jami’ai suka ce yana da nufin ƙarfafa tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa hadin gwiwa da aka rattaba hannu a kai a ranar Litinin wadda Adamu Abdullahi, Daraktan wayar da kan Jama’a, da Mustapha Hamisu Spy, Mataimaki kan harkokin Sadarwa ga Kwamishinan gidaje suka fitar.
A cikin wata sanarwa, gwamnati ta bayyana cewa shirin na nuna ƙudurin ta na inganta sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa da ke shiga Kano tare da ƙarfafa tsarin tsaro.
Yayin miƙa wuraren aikin ga ‘yan kwangila, Kwamishinan Gidaje ya ce kafa ƙofofin karɓar kuɗin hanya a manyan hanyoyin shiga birnin an yi shi ne bisa tsari domin ƙarfafa tsaro da tattalin arziƙi.
Ya buƙaci ‘yan kwangilar su bi ƙa’idojin aikin tare da kammala shi a kan lokaci, yana mai jaddada cewa hakan na da muhimmanci domin cimma sakamakon da ake so.
An cewar saz samar da ingantaccen sa ido a wuraren shiga birnin zai taimaka wajen dakile zirga-zirgar ababen hawa ba bisa ƙa’ida ba tare da kare rayuka da dukiyoyi.
Za a gina ƙofofin karɓar kuɗin ne a kan titunan Daura, Katsina, Gwarzo, Zaria, Maiduguri, Hadejia da Sa’adatu Rimi, waɗanda ke haɗa Kano da jihohin maƙwabta da sauran sassan ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa aikin zai ƙarfafa tsaro a cikin gida tare da samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga domin tallafa wa ci gaban ababen more rayuwa a faɗin jihar.













































