DA DUMI-DUMI: jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi hatsari

BREAKING 1
BREAKING 1

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya yi hatsari a Bauchi a ranar Larabar, inda ya raunata mutane shida, kamar yadda hukumar binciken haddura ta AIB ta bayyana.

Jirgin mai saukar ungulu ya taso ne daga Abuja amma AIB ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba a hadarin.

Hukumar ta ce hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya NAMA ce ta sanar da ita hatsarin kuma tuni aka fara gudanar da bincike.

“A ranar 26 ga Janairu, 2022, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) ta sanar da Ofishin Binciken Hatsarin Najeriya game da wani hatsarin da ya rutsa da wani jirgin sama kirar Bell 429 mai lamba 5N-MDA mallakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF),” inji sanarwar.

Yace. “Hatsarin ya faru ne a ranar 26 ga Janairu, 2022 da misalin karfe 7:30 na yamma a filin jirgin Bauchi.

“Jirgin NPF ya taso ne da misalin karfe 16:54 UTC zuwa Bauchi tare da mutane shida, yake gudu kan matakin 5,500ft. an samu raunuka amma babu wanda ya rasu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here