Gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwar wasu wuraren shakatawa da lambuna a jihar don sake ingantasu.
SolaceBase ta rawaito cewa galibin wuraren shakatawa na jama’a da lambuna a cikin jihar yanzu yawancin masu gudanar da kasuwanci suna mamaye da su.
Jihar ta ce kwato dukkanin wadannan cibiyoyin na da nufin sake kafa wani wurin shakatawa da ya dace da jama’a domin shakatawa da daidaita yanayin muhalli.
Karin labari: Bankin Heritage: NDIC ta fara biyan kudaden inshora ga masu ajiya miliyan 2.3
Kwamishinan Muhalli na Jihar, Alhaji Nasir Sule Garo ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taron manema labarai a wani bangare na gudanar da bukukuwan ranar muhalli ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware.
Kwamishinan ya ce gangamin dashen itatuwan da gwamnatin jihar ta kaddamar na da nufin dakile kalubalen sauyin yanayi da jihar ke fuskanta da Najeriya da ma duniya baki daya.
Kwamishinan ya kara da cewa, sauran ayyuka da nasarorin da gwamnatin jihar ta samu kan al’amuran muhalli tun daga farkon wannan gwamnati zuwa yau an samu ci gaba da dama ta fanni daban-daban.