Wike ya bai wa masu karya dokar amfani da filaye wa’adin kwanaki 14 su biya tara

Wike NBA 750x430

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa masu mallakar filaye da suka sauya amfani da su ba tare da izini ba, wa’adin kwanaki 14 domin su biya tarar Naira miliyan biyar.

Wannan umarni ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa minista kan hulɗa da jama’a da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar a birnin Abuja a ranar Lahadi.

Sanarwar ta bayyana cewa wa’adin zai fara aiki daga ranar 11 ga watan Nuwamba, kuma duk wanda bai biya cikin lokacin da aka kayyade ba, za a ɗauki matakin tilastawa daga hukumar gudanarwar babban birnin tarayya.

Olayinka ya bayyana cewa wuraren da abin ya shafa sun haɗa da titin Gana da titin Usuma a Maitama, titin Yakubu Gowon a Asokoro, titin Aminu Kano da titin Adetokunbo Ademola a Wuse II, titin Ladoke Akintola da titin Gimbiya.

Haka kuma wuraren sun haɗa da titin Onitsha a Garki II, titin Ogbomosho, titin Lafia, titin Yola, titin Abriba, titin Danbatta, titin Ringim da titin Ilorin a unguwar Garki I.

A cikin wannan wa’adin kwanaki 14, an umarci masu filayen da su kai takardun mallaka na asali tare da katin shaida zuwa sashen kula da filaye domin gyara izinin amfani da filayen, domin su karɓi sabbin takardun mallaka da za su nuna sabon nau’in amfani da fili na shekara 99.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sabbin takardun mallaka da za a bayar ba su shafi filaye da aka riga aka soke ko aka janye saboda rashin ci gaban fili, rashin biyan harajin ƙasa ko wasu dalilai ba.

Olayinka ya ƙara da cewa hukumar babban birnin tarayya ta sake duba tsarin amfani da filaye, inda ta bai wa masu sauya amfani da filaye ba tare da izini ba kwanaki 30 su biya tarar, amma lokacin ya ƙare sama da wata guda da ya gabata.

NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here