Ƙungiyar ma’aikatan da ba malamai a manyan makarantun kasar nan da ƙungiyoyi masu alaƙa da su (NASU) ta roƙi jami’an gwamnati da ta daina amfani da manufar “babu aiki, babu albashi” a matsayin hanyar tsoratar da ma’aikata.
Sakatare janar na NASU, Yarima Peters Adeyemi, ne ya yi wannan kira a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a birnin Abuja.
Adeyemi ya bayyana cewa barazanar da wasu jami’an gwamnati ke yi ta amfani da manufar tana nuna rashin adalci kuma tana sabawa ƙa’idodin dangantakar ma’aikata.
Ya ce an yi nufin tanadin sashe na 42(1)(a) na dokar rikicin ma’aikata domin tabbatar da daidaito, amma yanzu ana amfani da shi wajen hana halaccin yajin aiki.
Ya bayyana cewa yajin aiki, ba a yin shi cikin gaggawa, amma ana zuwa gare shi ne bayan an yi ƙoƙarin tattaunawa da gwamnati ta hanyoyin doka amma ba a sami sakamako ba.
Ya ƙara da cewa jami’an gwamnati kan jinkirta albashin ma’aikata ko karya yarjejeniya, amma su ne ke fara barazanar hukunci idan ma’aikata suka mayar da martani.
Adeyemi ya ce yin amfani da matakin “babu aiki, babu albashi” ba tare da duba manufar “babu albashi, babu aiki” ba, ba gaskiya ba ne, domin hakan yana sabawa ka’idar daidaito.
Ya kuma jaddada cewa ƙungiyar ƙwadago ta duniya (ILO) a cikin yarjejeniyoyin ta na 87 da 98 ta amince da yajin aiki a matsayin muhimmin ɓangare na ’yancin haɗin kai da tattaunawar ƙungiyoyi.
Ya bayyana cewa hukunta ma’aikata saboda shiga yajin aiki na halak yana sabawa ƙa’idodin ƙasa da ƙasa da dokokin ƙwadago na ƙasar nan.
Ya kuma ce, gwagwarmayar ma’aikata ba tawaye ba ce, illa dai neman adalci da mutunci.
Adeyemi ya ƙara da cewa babu wanda ya fi ma’aikacin Najeriya kishin ƙasa, domin duk da ƙarancin albashi da rashin cika alkawura, su ne ke ginawa da kuma tafiyar da ƙasa.
Ya kuma shawarci gwamnati ta girmama yarjejeniyoyi da ƙungiyoyin ma’aikata domin tabbatar da zaman lafiya a harkokin masana’antu, tare da bin doka, mutunta juna da tattaunawa don samun daidaitacciyar dangantakar aiki mai adalci.













































