Gwamnatin jihar Kano ta ce tana shirin kashe kimanin Naira biliyan 3.5 wajen bayar da tallafin karatu ga dalibai 550 domin yin karatun digiri na biyu a kasashen waje.
Dakta Yusuf Kofar-Mata, kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Kano, lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar jihar na mako-mako. Kofar-Mata ya ce daliban za su yi karatu a jami’o’i bakwai a Indiya da Uganda.
Kwamishinan ya ce an zabo mutane 550 daga cikin dalibai 1,250 da suka nemi tallafin