Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama Abuja, a ranar Talata ta jinkirta yanke hukunci kan wani roko da aka nemi ta dakatar da shari’ar cin hancin Naira biliyan 2.8 da ake tuhumar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da shi, har zuwa ranar da za a yanke hukunci na karshe a kan babbar kara.
Mai shari’a S.C. Oriji ne ya yanke wannan shawara a lokacin zaman sauraron karar da Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar, inda take karar Sirika, ’yarsa Fatima Hadi Sirika, da surukinsa Hamma Jalal Sule.
Hukumar EFCC ta gurfanar da wadanda ake karar ne kan tuhume-tuhume shida aka gyara da suka shafi zargin zamba a kwangilolin da ke da alaka da Al Buraq Global Investment Limited, wani kamfani da ake zargin yana da alaka da ’yarsa. EFCC ta zargi cewa kwangilolin da ake magana akai sun kai Naira 2.83 biliyan.
A zaman na ranar Talata, lauyan wanda ake kara na uku, Sanusi Musa (SAN), ya roki kotu ta hana masu gabatar da kara gabatar da karin shaida a shari’ar.
Haka kuma, ya roki kotu da ta yi watsi da duk wata shaida da zargin da aka riga aka gabatar gaban kotu, sannan ta wanke su daga tuhuma.
Musa ya ce masu gabatar da kara sun shigar da karar ne ba tare da yin cikakken bincike ba, don haka bai kamata a ba su damar ci gaba da shari’ar ba.
Sai dai lauyan masu kara, Rotimi Jacobs (SAN), ya yi soki da rokon, inda ya ce Dokar Shari’ar Laifuka ta 2015 ACJA ta ba da dama a gabatar da karin shaida da duk wani abu da ake zargi a kowane mataki kafin a yanke hukunci karshe.
Jacobs ya kara da cewa akwai hukunce-hukunce da dama na Kotun Ƙoli da Kotun Daukaka Kara da ke goyon bayan yarda da karin shaida a yayin shari’ar laifi da ke gudana.
A cikin hukuncinsa, Mai shari’a Oriji ya ce ko da yake Wanda ake kara na damar daga yin kalubale kafin yanke hukunci, batutuwan da ke cikin rokon suna da alaka ta kut da kut da babbar tuhuma dake gaban kotu.
“Wannan roko ba ya kalubalantar ingancin tuhuma. Duk da haka, batutuwan da rokon da ke ciki suna da alaka ta kut da kut da yanke hukunci kan tuhuma.
Saboda haka, a ganina, a hikimar shari’a zai fi dacewa a yi hukunci kan rokon tare da hukuncin karshe kan tuhumar bayan kammala shari’a, kuma na ba da umarni haka,” in ji shi.
Bayan haka sai ya dage shari’ar zuwa 10 ga Yuni, 2026, domin ci gaba da sauraron kara.












































