Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya janye kansa daga shari’o’i biyu da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar kan tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.
Mai Shari’a Egwuatu, wanda Babban Alƙalin Kotun Tarayya, Mai Shari’a John Tsoho, ya sake ba wa shari’ar kwanan nan, ya ce ya yanke shawarar janyewa daga shari’o’in ne saboda wasu dalilai na kashin kai da kuma domin tabbatar da adalci.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan an kira karar ta kwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da Malami domin a ambace ta.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun da farko shari’o’in na gaban Mai Shari’a Emeka Nwite, wanda ya zauna a matsayin alƙalin hutu a lokacin hutun Kirsimeti.













































