Shettima ya bar Abuja zuwa Ethiopia domin halartar taron kungiyar tarayyar Afirka

IMG 20260212 WA0005 750x430

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja ranar Alhamis zuwa Addis Ababa, na kasar Ethiopia domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) na 2026.

KoKamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa taken taron shi ne: “Tabbatar da wadatar ruwa mai ɗorewa da ingantattun hanyoyin tsafta domin cimma manufofin a 2063.”

Taron zai mayar da hankali kan ƙarfafa ƙudurin nahiyar Afirka wajen kula da ruwa mai ɗorewa, inganta tsarin tsafta, da kuma cimma burin ci gaba da ke kunshe a tsarin Agenda 2063 na AU.

Yayin da yake Addis Ababa, Shettima zai halarci zama na 39 na Babban Taron Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci na AU tare da sauran shugabannin Afirka.

Haka kuma zai halarci zama na 30 na Babban Taro da za a gudanar daga ranar 14 zuwa 15 ga Fabrairu.

Mataimakin shugaban ƙasar zai shiga manyan taruka da kuma ganawa da shugabannin siyasa da na kasuwanci domin ƙarfafa dangantakar diflomasiyya, tattalin arziki da dabarun hulɗa tsakanin Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar.

Ana sa ran Shettima, wanda ya tafi tare da ministoci da manyan jami’an gwamnati, zai dawo Najeriya bayan kammala ayyukansa a Addis Ababa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here