Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu mata biyu sub rasa rayukansu a wani kududdufi da ke karamar hukumar Gezawa a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Laraba.
“Mun samu kiran gaggawa a safiyar ranar Talata da misalin karfe 11:15 na safe daga kungiyar ‘yan banga a Gezawa cewa mata sun nutse a cikin wani kududdufi.
‘Yan uwan wadanda abin ya shafa sun sanar da kungiyar cewa matan suna aiki a wani kamfanin sarrafa Zobo.
Karanta: Gwamnatin Kano ta samar da dokar kare muhalli don yaƙi da gurɓatar yanayi
“Sun ce matan sun je kududdufin ne domin su wanke jikin su bayan sun tashi aiki.
“Mun aika da tawagar mu cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru kuma muka kwaso gawarwakin daga kududdufin” inji shi.
Ya ce an mika gawarwakinsu ga wani dan sanda Musa Garba, a sashin ‘yan sanda na Gezawa.
Saminu ya shawarci jama’a da su daina zuwa kusa da kududdufi da koguna domin hana afkuwar lamarin. (NAN)












































