Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) a hukumance ta ba da umarnin aiwatar da cikakken yarjejeniyar cinikin danyen mai sa Naira wanda aka dakatar a matatun man kasar nan.
Ma’aikatar Kudi ta tarayya ta bayyana hakan ne a kan ofishinta na X yau Laraba, inda ta yiwa yarjejeniyar take da “Sabuntawa cinikin danyen mai da tattalin Arziki bisa tsarin amfani da Naira,”.
A cewar sanarwar, kashi na farko na yarjejeniyar ta tsawon watanni shida ta shafi gwamnatin tarayya, kamfanin mai na Najeriya, da matatar Man Dangote ya kare a ranar 31 ga Maris, 2025.
Ba a sake sabunta ta ba, kuma matatar Dangote ta daina sayarwa da tace man fetur a naira saboda rashin sabunta cinikin danyen mai a naira.
A cikin wani sabon bayani da aka fitar a ranar Laraba, kwamitin ya ce manufar ba ta wucin gadi ba ce, amma shiri ne na dogon lokaci domin rage dogaron da Najeriya ke yi da kudaden waje na man fetur.
Hakan ya biyo bayan wani muhimmin taro da aka gudanar a ranar Talata domin duba ci gaban da aka samu tare da tunkarar batutuwan da ke ci gaba da gudana.
Karin bayani na tafe……