Yadda jami’an tsaro suka yi yunkurin kama El-Rufai a filin jirgi – Mataimaki

IMG 9015 750x430

Mai taimaka wa Nasir El-Rufai kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce jami’an tsaro sun yi yunkurin kama tsohon gwamnan Jihar Kaduna a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da yake dawowa daga birnin Alkahira na kasar Masar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Adekeye ya ce jami’an sun tunkari El-Rufai ne jim kadan bayan ya sauka daga jirgi ranar Laraba, amma ya ki binsu saboda babu wata takardar gayyata a hukumance.

“Jami’an tsaro sun yi yunkurin kama Malam Nasir El-Rufai yayin da ya iso daga Alkahira. Malam El-Rufai ya ki binsu ba tare da takardar gayyata ba. Sai dai sun kwace fasfo dinsa na kasa da kasa daga hannun wani mataimaki,” in ji shi.

Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya bayyana lamarin a matsayin “keta kundin tsarin mulki karara” da kuma “wuce gona da iri na bangaren zartarwa,” yana zargin jami’an Hukumar DSS da yunkurin tsare tsohon gwamnan ba tare da sammaci ko gayyata a hukumance ba.

A cewar wata sanarwa da Akpan ya fitar, El-Rufai ya nemi a nuna masa takardar gayyata amma ba a gabatar masa da ita ba.

Ya ce daga nan jami’an suka kwace fasfo dinsa daga hannun mataimaki, abin da ya kira sata da kuma take hakkin mallaka.

Akpan ya ce a watan Disamba 2025 ne EFCC ta kai takardar gayyata gidan El-Rufai yayin da yake kasashen waje, wanda tawagarsa ta dauka a matsayin ba mai yiwuwa ba.

Ya ce sun bai wa EFCC tabbacin hadin kai tare da sanar da hukumar a ranar 11 ga Fabrairu, 2026 cewa El-Rufai zai je ofishinsu da kansa da karfe 10:00 na safe ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026.

Sai dai duk da wannan alkawari, an yi yunkurin kama shi.

Lauyan ya lissafa hakkoki da aka ce an keta, ciki har da ‘yancin kai, sauraron shari’a cikin adalci, mutunci, ‘yancin zirga-zirga da kuma hakkin mallaka.

Ya bukaci a mayar da fasfo din nan take, a dakatar da duk wani yunkurin tsare shi ba bisa ka’ida ba, tare da neman afuwa a hukumance.

Ya kara da cewa El-Rufai ba zai taba gudun hukuma ba kuma zai amsa duk wata gayyata ta doka ba tare da sharadi ba.

Lamarin na zuwa ne bayan El-Rufai ya yi ikirarin cewa zai iya fuskantar kame ta siyasa idan ya dawo Najeriya, yana mai cewa wasu daga cikin makusantansa ana tsare da su bayan sukar gwamnatin da ke kan mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here