Mambobin Hizbullah hudu sun kwanta dama a wani hari ta sama

SOJOJIN ISRA'ILA
SOJOJIN ISRA'ILA

Kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran ta ce an kashe mambobinta 4 a wani hari da kafofin yada labarai suka ce Isra’ila ta kai ta sama kan kauyen Naqoura.

Gidan Talabijin na Al-Manar ya ce mutanen hudu sun yi shahada kuma a cewar wata sanarwa da aka fitar a daren Laraba, daga cikin wadanda suka mutu akwai jami’in kungiyar Hizbullah.

Karanta wannan: ‘Yan Hisbah sun kama wata mota makare da Barasa a Kano

Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ruwaito jirgin na Isra’ila ya jefa bom kan wani gini mai hawa uku lamarin da ya sanya ginin ya ruguje baki daya.

Ya kuma ce wasu fararen hula tara sun jikkata sakamakon harin.

Jaridar The Times ta Isra’ila ta ce adadin mambobin Hizbullah da aka kashe tun fara yakin a watan Oktoba sun zarce 150.

Karanta wannan: Hukumar kula da zirga-zirgar jiargen Kasa za ta fara Jigilar dare

Isra’ila da Hizbullah sun shafe watanni suna kai wa junansu hare-hare.

Zuwa yanzu, Isra’ila ba ta ce komai ba a kan lamarin.

A daren Laraba, rundunar sojin Isra’ila ta wallafa wani bidiyo a shafin intanet wanda ya nuna tana kai hare-hare kan cibiyoyin Hizbullah a yankunan Lebanon.

Karanta wannan: Zargin almundahana: EFCC ta kama shugabar hukumar NSIP, Halima Shehu

Hoton bidiyon ya nuna yadda aka kai hari kan gine-gine da dama daga bisani kuma aka ga fashewar abubuwa da hayaki na tashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here