Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya tarbi manyan jiga-jigan kungiyar Kwankwasiyya Ulama Forum da sauran kungiyoyin siyasa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A wani sako da ya wallafa a kafafen sada zumunta a ranar Asabar, Jibrin ya bayyana cewa ya tarbi Malam Yahaya Abdulkadir Aliyu, Sakataren kungiyar Kwankwasiyya Ulama Forum, tare da shugabannin zartarwa 23, yayin da suka koma APC a hukumance.
Bugu da kari, Mahbub Nuhu Wali, dan uwan gwamnan jihar Kano, shi ma ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa a ziyarar da suka kaiwa Jibrin a zauren majalisar a ranar Juma’a, sabbin ‘yan jam’iyyar APC sun yi watsi da jajayen hular da suke sanye da su wadda take nuna alamar tafiyar Kwankwasiyya.
Karin karatu: Atiku yayi watsi da rahotannin sauya sheka Daga jam’iyyar sa ta PDP
Daga ofishin sa, sun zarce da shi zuwa wani taro inda suka shiga gamayyar kungiyoyin goyon bayan Atiku Abubakar na zaben 2023 daga jihohin Arewa 19.
Bayan kammala taron, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Daga cikinsu akwai jiga-jigan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) guda biyu daga karamar hukumar Gwale ta jihar Kano, Mahmoud Salisu Gwale da Farouk Ahmed Gwale.
Da yake karbar sabbin mambobin, Jibrin ya jaddada kudirinsa na yiwa al’ummar yankin Kano ta Arewa hidima da sauran su, ba tare da la’akari da siyasarsu ba.