Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce ba shi da wani shiri na ficewa daga jam’iyyar sa ta People’s Democratic Party (PDP).
A baya-bayan nan dai an samu rahotannin cewa Atiku ya kammala yunkurin shiga jam’iyyar (SDP).
Da yake mayar da martani ga rahotannin a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, ofishin yada labarai na Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar yana nan kuma zai ci gaba da zama dan PDP na gaskiya.
Ofishin yada labaran ya bayyana rahotannin a matsayin “karya”, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da su.
Karanta: NNPP za ta kayar da APC da PDP a zaɓen 2027 – Kwankwaso
Ofishin yada labaran ya ce Abubakar zai ci gaba da yin kira ga hadakar jam’iyyun siyasa na adawa a Najeriya kafin zaben 2027 don kawar da jam’iyyar APC mai mulki.
Ya kuma jaddada cewa ikirarin sauya shekar wani yunkuri ne na rudar da ‘yan Najeriya game da girman babbar kungiyar da ke aikin ceto Najeriya daga hannun APC.