ADP: Sha’aban Sharada ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kano

Shaaban Sharada 2 708x430 1
Shaaban Sharada 2 708x430 1

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni ta Jihar Kano, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kano karkashin jam’iyyar ADP a hukumance.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Sha’aban Sharada, wanda tsohon mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kan harkokin yada labarai, shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilan Kan sha’anin tsaro da kuma leken asiri.

A ranar Asabar ne dan takarar gwamnan na Jam’iyyar ta ADP, ya yi zagayen manyan titunan cikin birnin Kano domin bayyana aniyarsa yayin da ayarin motocin suka tashi daga ofishin yakin neman zaben sa dake kan titin Maiduguri zuwa Sani Abacha Youth Center.

Daruruwan masu ababen hawa ne suka bi ayarin Dan takarar lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano, yayin da wasu ke dauke da allunan dan takarar gwamnan.

Shaaban Ibrahim Sharada, wanda a baya ya sha fafatawa da Gwamna Abdullahi Ganduje a lokacin da yake jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar ne bayan da ya kasa samun tikitin takarar gwamna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here