Ya zama dole a mutunta Yan Jarida a Najeriya- Gwamna Bala Mohammed

Bala Mohammed new
Bala Mohammed new

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed Abdulkadir, ya ce ‘yan jarida da sauran masu aikin yada labarai ne mutanen da suka fi kowa daraja a Najeriya.

Mohammed, ya bayyana haka ne a Bauchi yayin da yake mika kyautar sabbin motoci kirar Toyota Hiace guda biyu ga Yan Jaridar gidan gwamnati da kuma kungiyar ‘yan jarida ta kasa (wato NUJ) a jihar.

A cewarsa, masu aikin yada labarai a ko da yaushe suna fama da takura da kalubalen tattara labarai Kuma duk da Irin gudunmawa da suke bayarwa ga al’umma amma ba su da albashi da Mai kyau.

Ya kara da cewa ‘yan jarida suna shan wahala matuka duk da cewa sun fi kowa bada gudunmawa wajen ci gaban al’ummar Kasa.

Mohammed, wanda ya ce ya bayar da motocin ne domin nuna cewa aikin jarida da ‘yan jarida na da mutunci, ya kara da cewa dole ne a mutunta su tare da karfafa musu gwiwa su yi aiki yadda ya kamata don samar da yanayi mai kyau.

Ya ce idan aka yi la’akhari da ayyukan su, dole ne a ba wa ‘yan jarida daraja ta fuskar gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.

Ya ce hakan zai sa aikin ya kasance mai daraja ta yadda ‘yan jarida za su samu albashi da alawus-alawus da sauran abubuwan jin dadin rayuwa.

Ya jaddada alkawarin sake gyara sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Kasa a jihar kafin cikar wa’adin mulkin sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here