Dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP a jihar Kano, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya yi alkawarin tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomin jihar idan har aka zabe shi a matsayin gwamna a 2023.
Sharada ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake bayyana takararsa a wani gagarumin biki da aka gudanar ranar asabar a cibiyar matasa ta Sani Abacha da ke Kano.
Da yake jawabi ga dimbin jama’a, Sha’aban Sharada ya ce a da kananan hukumomi sun kasance wurin da talakawa ke jin tasirin gwamnati ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa tun daga tushe.
A cewarsa, yanzu haka kansilolin sun zama abin tausayi saboda gwamnatin jihar bata fitar musu kason kudaden da ake ba su.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Sharada ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta bullo da wani abin da ya kira “stabilization account”, inda ake karkatar da kudaden kananan hukumomin da ake amfani da su wajen harkokin siyasa.
Ya ce idan ya zama gwamnan jihar, zai tabbatar da cewa kananan hukumomi suna samun kason su na tarayya a wani yunkuri na aiwatar da ayyuka, wanda zai taimaka wajen rage radadin talauci a jihar.
Sharada wanda mamba ne mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano a majalisar wakilan Tarayya, ya kuma yi alkawarin samar da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a kowace shiyya na kananan hukumomi 44 dake jihar.
Sha’aban Sharada, wanda shi ne Shugaban Kwamitin tsaro na Majalisar, ya ce Jam’iyyar ADP, duk da cewa sabuwa ce, amma tana samun gagarumin goyon baya a Kano.
Ya kuma yi alkawarin bunkasa fannin ilimi a jihar, inda ya ce, “tambarin babbar jam’iyyar mu, wanda littafi ne, na nufin za mu sake dawo da martabar bangaren ilimi a Kano. Za Kuma mu samar da ingantaccen tsarin ilimi don matasan mu masu tasowa su zama masu amfani a nan gaba.”













































