Barau ya tarbi dan takarar mataimakin shugaban kasa na SDP da dan takarar gwamnan Kano, da sauran su zuwa APC

WhatsApp Image 2025 03 19 at 01.43.44 750x430

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) 2023, Engr. Yusuf Buhari, da dan takarar gwamnan jihar Kano, Bala Muhammad Gwagwarwa da mambobin kwamitin ayyuka na jihar Kano, shugabannin kananan hukumomi 38 da sakatarori, da kuma wasu tsaffin ‘yan takarar majalisar wakilai da ta wakilai da dama sun fice daga jam’iyyar su zuwa APC.

A cewar wani sako da aka tabbatar a kafafen sada zumunta na mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I. Jibrin a ranar Talata, ya ce wannan gagarumin sauyin sheka ya nuna babban koma-bayan siyasa ne, kuma tare da isar da sako na manufar yin amfani da jam’iyyar SDP a matsayin dandalin kalubalantar jam’iyyar APC a 2027.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, sakon ya kara da cewa: ‘’Wannan gagarumin taron da aka yi a otal din REIZ Continental da ke Abuja ya tarbi ficewar dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar SDP a 2023, Engr. Yusuf Buhari, dan takarar gwamnan jihar Kano, Bala Muhammad Gwagwarwa, mambobin kwamitin ayyuka na jihar Kano, shugabannin kananan hukumomi 38 da sakatarorinsu, da kuma wasu tsoffin ‘yan takarar majalisar wakilai da ta wakilai.

Karin karatu: Kamata ya yi majalisar dokoki ta kasa ta amince da dokar ta bacin da Tinubu ya kafa a Rivers – Abaribe

Sanarwar ta ce wadanda suka yi imanin za su iya amfani da SDP don biyan bukatun kansu, an yi watsi da su kai tsaye, domin a halin yanzu jiga-jigan jam’iyyar SDP sun hade da APC a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here