Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta sake tsige Julius Abure daga mukamin shugaban jam’iyyar Labour Party ta ƙasa, tare da tabbatar da Sanata Esther Nenadi Usman a matsayin halastacciyar shugabar rikon kwarya ta jam’iyyar.
Kotun, karkashin jagorancin Mai shari’a Peter Lifu, ta jingina hukuncinta ne da hukuncin kotun koli da aka yanke a ranar 4 ga Afrilu, 2025, inda ta ayyana cewa Nenadi Usman ce ke da ikon jagorantar jam’iyyar a halin yanzu.
Biyo bayan hakan, kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da ta gaggauta amincewa da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar Labour Party karkashin jagorancin Nenadi Usman a matsayin sahihin shugabanci, har sai jam’iyyar ta gudanar da babban taron ƙasa.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da aka shigar a gaban kotu mai lamba THC/ABJ/CS/2262/2025, wadda Nenadi Usman ta gabatar, inda aka kuma sanya Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya a matsayin wadda ake ƙara a shari’ar.
Kotun ta bayyana cewa wa’adin shugabancin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar ya riga ya ƙare, tare da jaddada cewa kafa kwamitin rikon kwarya ya zama dole ne sakamakon umarnin kotun koli, ba batun cikin gida na jam’iyya kaɗai ba.
Idan za a iya tunawa, bayan rikicin shugabanci da ya girgiza jam’iyyar Labour Party, kwamitin zartarwa na ƙasa ya yanke shawarar tsige Abure, inda aka kafa kwamitin rikon kwarya mai mambobi 29 karkashin jagorancin Nenadi Usman, matakin da aka dauka a wani taron manyan masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Umuahia, Jihar Abia.
Kotun koli ta riga ta soke hukuncin kotun ƙasa da kotun ɗaukaka ƙara da suka amince da Abure, tare da jaddada cewa jam’iyyun siyasa su rika bin dokokinsu wajen nada shugabanni, kuma duk jami’in da wa’adinsa ya ƙare ya kamata ya sauka daga mukaminsa.













































