Majalisar dattawa ta ce zata fara tantance mimistoci 28 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike mata da sunayen su.
Kakakin majalisar, Sanata Adeyemi Adaramodu ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Alhamis bayan an karanta sunayen a gaban majalisar.
Adaramodu ya ce duk da cewa majalisar bai kamata ta zauna ranar Litinin ba, amma saboda muhimmancin akin shi isa zata zauna ranar Litinin.
Ya kuma tabbatar da cewa tantancewar zata gudana ba tare da wani matsala ba.













































