Mafi Karancin Albashi: Tinubu Zai Gana Da Kungiyar kwadago

created by photogrid
created by photogrid

Shugaban kasa Bola Tinubu zai gana da kungiyar kwadago a Abuja ranar Alhamis domin ci gaba da tattaunawa kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata a Najeriya.

Wata majiya mai karfi ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa shugaban kasar ya gayyaci shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da ‘Trade Union Congress’ (TUC) zuwa taron da ake sa ran za a yi a fadar Aso Villa da ke babban birnin kasar.

Ana sa ran shugaban kasar zai yanke shawara kan kudirin ₦62,000 na gwamnati da bangaren kamfanoni masu zaman kansu; da kuma bukatar ₦250,000 na Kungiyar Kwadago.

Taron na ranar Alhamis na zuwa ne kimanin wata guda bayan da shugaban kasar ya bayyana a jawabinsa na ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yunin 2024 cewa nan ba da jimawa ba za a aika da wani kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here