Dan majalisar wakilai, Akinremi ya rasu yana da shekaru 51

Akinremi

Majalisar wakilan Najeriya ta sanar da rasuwar Hon. Olaide Adewale Akinremi, wanda aka fi sani da Jagaban, wanda ya wakilci Ibadan ta Arewa a karkashin tutar jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Hon Akin Rotimi, ya fitar  ya ce dan majalisar ya kasan ce fitacce kuma jajirtatce a majalisa ta 10.

Akinremi shine shugaban kwamitin majalisar kan cibiyoyin binciken kimiyya na Najeriya.

Ya rasu a safiyar yau Laraba, 10 ga Yuli, 2024, bayan yar gajeriyar rashin lafiya. Yana da shekaru 51.

Sanarwar ta kara da cewa, “Har zuwa rasuwarsa, dan majalisar Oyo ya kasance mai kwazo da ya shahara da jajircewarsa don kawo ci gaban jama’ar da yake wakilta da kuma kasa baki daya.

“Akinremi ya kasance dan siyasa mai kishin kasa,ya kuma kyautata alakar sa da sauran yan majalisa don kawo cigaba mai dorewa a Najeriya”

Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da rashin mutuwar dan majalisar.

“Majalisar wakilai baki daya ta yi alhinin wannan gagarumin rashi tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan Akinremi, da ‘yan majalisar tarayya na Ibadan ta Arewa, gwamnati, al’ummar jihar Oyo, da kuma daukacin yan jam’iyyar APCA.“

“Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya baiwa iyalansa da masoyansa ikon jure wannan rashi mara misaltuwa. Allah ya jikansa da rahama.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here